in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata Sin da Afrika su hada karfi domin cimma burin ci gaba tare
2015-07-01 11:13:52 cri

Kasar Sin da kasashen Afrika ya kamata su hada karfinsu domin ganin sun tabbatar da zaman lafiya, da cimma burinsu na ci gaba da wadatar dukkan al'ummomin duniya, in ji mista Kuang Weilin, jakadan kasar Sin dake kungiyar tarayyar Afrika (AU). Ofishin jakadancin kasar Sin da ke Habasha da cibiyar nazarin zaman lafiya da tsaro ta jami'ar Addis Abeba sun shirya cikin hadin gwiwa a ranar Talata da wani taron kara wa juna sani a ofishin jakadancin kasar Sin dake Addis Abeba, hedkwatar wannan kasa da ke gabashin Afrika, domin murnar cikon shekaru 70 da samun nasara kan yaki da Fascist a lokacin yakin duniya na biyu.

Taron kara wa juna sani ya shafi batutuwa daban daban kamar gudunmuwar Sin da Afrika ga yaki da Fascist, da ma kuma munanan sakamakon yakin duniya na biyu bisa tsarin duniya.

Da yake jawabi a yayin taron, mista Kuang ya bayyana cewa, an samu manyan sauye sauye a cikin al'ummomin duniya da duniya baki daya a tsawon shekaru 70 da suka gabata.

Sin da Afrika sun taso kamar manyan masu karfi biyu a dandalin kasa da kasa, in ji jakadan kasar Sin. Tare da jaddada cewa, kasar Sin da Afrika ya kamata su hada karfi da karfe tare domin sauke nauyin da ke wuyansu na tarihi na gina wani tsarin duniya mai armashi, da zaman lafiya cikin karko da wadata tare. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China