Wakilai daga kasashen Sin da Afrika da kuma bankin duniya a ranar Talatan nan suka yi alkawarin kokarta hadin gwiwwa a bangaren masana'antu tsakanin su domin inganta ci gaban tattalain arziki, a lokacin taron yini biyu da ya gudana a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.
Mataimakiyar ministar kudi ta kasar Sin Liu Jianhua ta ce, yadda 'yan kasuwan kasar Sin suke zuba jari a kasashen Afrika da sauran kasashen waje, hakan na kara jawo hankalin fasaha a kan harkokin kudi, sadarwa ta zamani da ci gaba, don haka akwai matukar bukatar hadin gwiwwa.
Ta ce, kasar Sin a shirye take ta taimaki kasashen Afrika wajen gina kayayyakin more rayuwar su, a cimma burin samar da masana'antu ta rage matsin a bangaren kudi, sadarwa ta zamani da ayyukan kwadago na jama'a a nahiyar.
Haka kuma Madam Liu ta sanar da cewa, kasar Sin za ta kara adadin hadin gwiwwarta da sauran hukumomin duniya kamar bankin duniya a lokacin aikinta da kasashen nahiyar ta Afrika. Ta tabbatar da cewar, yanzu haka kasar ta Sin tana shirin kafa wata gidauniya ta kudi har dala miliyan 50, tare da bankin duniya domin taimakawa ayyukan ci gaba a yankunan dake tasowa da suka hada da Afrika.
A cewar wata kididdiga da Sin ta kasance kan gaban sauran kasashen duniya wajen huldar kasuwanci da Afrika na tsawon shekaru 6 a jere, inda adadin ciniki a tsakanin su ya kai dala biliyan 222. A shekara ta 2014, yawan jarin da Sin ta zuba a nahiyar ya kai dala biliyan 4 wato ya karu da kashi 14% ke nan daga shekarar dake gaban wannan. A kalla akwai manya da matsakaitan kamfanoni na kasar Sin guda 2,500 da suka yi ragistan aiki a Afrika a bangarori da dama. (Fatimah)