Kasar Sin ta ba da rancen kudi mai sassauci dalar Amurka biliyan 30 ga kasashen Afrika domin tallafawa muhimman ayyukan da suka hada da gine ginen ababen more rayuwa, noma, masana'antun kere kere tsakanin shekarar 2012 da shekarar 2015.
Wannan ne adadin da aka rubunya har sau biyu da gwamnatin kasar Sin ta fitar, domin hakan a tsawon shekaru goma da suka biyo bayan kaddamar dandalin dangantakar Sin da Afrika (FOCAC) a shekarar 2000, in ji jakadan kasar Sin Yang Min dake Madagascar a ranar Litinin a yayin wani zaman taro da ma'aikatar harkokin wajen kasar Madagascar ta shirya da kuma aka sanya bisa taken "Bunkasa huldar dangantaka da abokantaka tsakanin Sin da Afrika tare da kwarin gwiwar FOCAC.
FOCAC, wani dandali ne na shawarwari, tuntubar juna da kuma dangantaka tsakanin Sin da Afrika. Taron ministoci karo na shida na dandalin Sin da Afrika zai gudana a kasar Afrika ta Kudu a karshen wannan shekarar.
Tun lokacin kafa FOCAC, gwamnatin kasar Sin ta kafa wani asusun ci gaban Sin da Afrika tare da dalar Amurka biliyan 605 tsakanin shekarar 2001 da shekarar 2009, ta soke basusuka 312 na kasashen Afrika 35 wadanda bashi ya yi wa katutu, da ya tasamma kimanin dalar Amurka biliyan 3, wanda daga cikinsu miliyan 56 na kasar Madagascar, in ji jami'in diplomasiyyar kasar Sin.
Bisa shirin FOCAC, kasar Sin ta kafa cibiyoyin ba da jagoranci a Afrika 20 kan noma a cikin kasashen Afrika, har da Madagascar. Tun daga shekarar 2001, fiye da likitocin kasar Sin 200 suka je kasashen Afrika bisa tsarin tawagogin likitanci, asibitoci 54 da cibiyoyin yaki da zazzabin cizon sauro, an kafa su tare da taimakon gwamnatin kasar Sin, kuma fiye da ma'aikatan Afrika dubu 40 suka samu horo a kasar Sin. (Maman Ada)