A nasa bangaren, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga shugaba Sirleaf, inda ya bayyana cewa, kasar Sin aminiyar abokiyar kasar Liberia ce, don haka ya kamata Sin ta dauki alhakin taimaka wa kasashen Afirka dake fama da cutar Ebola wajen yaki da cutar.
A halin yanzu kuma, bisa jagorancin shugaba Sirleaf, gwamnati da jama'ar kasar Liberia sun yi nasarar yaki da cutar Ebola,har aka kawo karshen yaduwarta a duk fadin kasar, dangane da haka, gwamnati da jama'ar kasar Sin sun taya kasar murna da kuma yabo matuka kan wannan nasara.
Bugu da kari, kasar Sin na son taimaka wa kasar Liberia kan yadda za a farfado da tattalin arziki da yanayin zaman takewar al'umma, bayan da aka kawo karshen yaduwar cutar Ebola a kasar, haka kuma, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, domin tallafawa jama'ar kasashen biyu. (Maryam)