'yan sandan su 140 wadanda suka kunshi mata 5 sun kasance rukuni na uku da kasar Sin ta tura zuwa Liberia dake yammacin Afrika. Kasar Sin ta tura rukunin farko na 'yan sandan kwantar da tarzoman ta da suka hadu da ma'aikatan zaman lafiya na MDD a watan Oktobar 2013.
A yanzu haka akwai 'yan sandan kwantar da tarzoma Sinawa 173 a cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen da suka hada da Liberiya, Sudan ta kudu, Cyprus da kuma cibiyoyin MDD kamar yadda sanarwar ta bayyana.(Fatimah)