Kamfanin Huawei na kasar Sin da ya shahara wajen samar da bayanai da harkokin sadarwa na zamani (ICT) zai fadada shirinsa na samar da horo ga Afirka, a wani mataki na bunkasa samar da bayanai da harkokin sadarwa na zamani a nahiyar.
Mataimakin shugaban kamfanin Charles Ding ya bayyana cewa, shirin zai bai wa daliban nahiyar sama da 1,000 damar samun horo a wannan fannin a kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa.
Charles Ding wanda ya bayyana hakan a yayin taron dandalin tattalin arziki na duniya game da Afirka na wannan shekara da ke gudana a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu ya ce, akwai bukatar gwamnatocin nahiyar Afirka su kara bullo da hanyoyin yin hadin gwiwa da sauran kasashe ko fannoni.
Bugu da kari, kamata ya yi nahiyar ta kara zuba jari a harkokin sadarwa na zamani, tare da horas da mutane masu basira, matakin da ya ce zai taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi, bunkasa tattalin aztiki da inganta makomar nahiyar ta Afirka.(Ibrahim)