in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na hadin gwiwa da kasashen Afirka wajen yaki da safarar sassan dabbobi
2015-05-15 10:07:59 cri

Jakadan kasar Sin a Habasha La Yifan, ya ce, kasarsa na ci gaba da hadin gwiwa da kasashen Afirka, wajen yaki da mummunar sana'ar nan ta cinikayyar sassan jikin dabbobi, musamman ma hauren giwa.

Da yake jawabi yayin wani taron karawa juna sani, game da fataucin sassan jikin dabbobin daji da ya gudana a birnin Adis Ababan kasar Habasha, Mr. La ya ce, kasar Sin na daukar karin matakai daban daban, domin dakile wannan haramtacciyar sana'a, da kuma baiwa namun daji kariya.

Shi kuwa a nasa jawabi, shugaban sashen kula da cinikayyar sassan jikin namun daji ta binciken yanar gizo na kasar Sin Zhou Fei, cewa ya yi, an shirya taron na wannan karo ne, domin fadakar da Sinawa dake zaune a kasar Habasha, kan muhimman batutuwan da suka jibanci wannan batu na fataucin sassan dabbobi daga nahiyar Afirka. Ya ce, wannan shi ne karo na biyu, da aka gudanar da wannan taro, tun bayan wanda ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya a bara.

A nasa bangare, babban daraktan hukumar kare gandun daji na kasar Habasha Dawud Mume, ya ce, Habasha ta zamo cibiyar da masu fataucin sassan namun daji ke amfani da ita. Kana mahukuntan kasar sun sha cafke irin wadannan hajoji daga masu fataucin su a kasar. A hannu guda kuma gwamnatin kasar na kara daukar matakan dakile wannan mummunar sana'a, wadda aka yi amannar cewa, tana da alaka da kungiyoyin masu aikata laifuka, kamar masu safarar miyagun kwayoyi, da na 'yan ta'adda da kuma masu safarar bil adama. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China