Shugabar hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Madam Nkosazana Dlimini Zuma ta yaba da irin goyon bayan da kasar Sin ta baiwa nahiyar Afirka a gwagwarmayar da ta yi ta neman 'yanci daga Turawan mulkin mallaka.
Madam Zuma wadda ta bayyana hakan yayin da take jawabi a wani taron hadin gwiwar Sin da Afirka na kwanaki biyu da ya gudana a jami'ar Cape Town ta kuma bayyana cewa, kasar ta Sin ta baiwa nahiyar tallafin lokacin da aka samu barkewar cutar Ebola na baya-bayan nan a wasu sassan nahiyar.
Bugu da kari, Madam Zuma ta ce, kasar Sin ta ci gaba da agazawa nahiyar wajen raya kayayyakin more rayuwa da horas da dubban 'yan Afirka a fannoni dabam-dabam da kuma samar da tsaro.
Ta ce, nahiyar Afirka za ta yi koyi daga fasahohin kasar Sin a bangaren raya masana'antu, da gina muhimman kayayyakin more rayuwa, horas da ma'aikata da samar da zaman lafiya da tsaro, yayin da kungiyar AU ke kokarin cimma burin ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.
Yanzu dai hadin gwiwar sassan biyu na ci gaba da bunkasa cikin sauri.(Ibrahim)