in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a yi taron tattalin arzikin Afrika na shekara-shekara a Habasha
2014-06-24 10:20:59 cri

Hukumar MDD a kan tattalin arzikin Afrika ta ce, ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron attalin arzikin Afrika na shekara-shekara AEC, wanda za'a yi daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Nuwamba mai zuwa, a babban birnin Habasha Addis Ababa.

Hukumar MDD a kan tattalin arzikin Afrika, wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta kara da cewar, dama ana gudanar da irin wannan taron, tare da hadin gwiwar bankin raya kasashen Afrika AFDB, da kuma shirin raya kasashe na MDD UNDP.

Taken taron na wannan shekara shi ne "Ayyukan hannu, fasaha da kirkire-kirkire domin bunkasar tattalin arziki."

Taron tattalin arzikin na Afrika, wani babban dandali ne da yake hada mutane da yawa, wadanda suka hada da kwararrun malamai, jami'o'i, da kuma kwararru a kan ci gaba a fagen tattalin arziki, ana haduwa domin tattaunawa, da musayar ra'ayoyi a kan muhimman kalubale dake fuskantar Afrika. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China