in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya karbi hannayen jarin kamfanin AML
2015-04-24 10:05:45 cri

Hamshakin kamfanin tama da karafa na kasar Sin mai suna Shandong Iron and Steel group ya karbi ragowar kashi 75 cikin100 na hannayen jarin kamfanin sarrafa karafa na Tonkolili da ke Saliyo.

Wata sanarwa da aka ba da a jiya na nuna cewa, yarjejeniyar da ta kunshi karin dala miliyan 170 ta baiwa babban kamfanin na kasar Sin karin ikon fada a ji a kamfanin sarrafa karafa na gundumar Tonkokili da ke arewacin kasar ta Saliyo.

Bugu da kari wannan na nuna cewa, kamfanin na sarrafa tama da karafa na Shandong zai fara mallakar albarkatun kamfanin hadin gwiwar kamfanin AML na tashoshin jiragen ruwa da na kasa.

Canjin ikon harkokin kamfanin shi ne mafi girma a harkokin zuba jari a bangaren hako ma'adinai a kasar Saliyo, bayan da aka shafe watanni kamfanin na AML mallakar wani dan kasuwa mai suna Frank Timis na fuskantar matsalolin kudi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China