Asusun ba da agajin hadin gwiwa ga Sudan, wani tsarin hadin gwiwa na tattara kudi da MDD ta kafa a shekarar 2005 ya samu taimakon kudin da yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 60.
Hukumar daidaita harkokin jin kai ta MDD ta bayyana a ranar Litinin a cikin wata sanarwar da aka samu a birnin Nairobi cewa, wadannan kudade za su taimaka wajen tallafawa kungiyoyin agaji da za su amfani da su yayin yayayin kaka a kasar Sudan ta Kudu domin isar da taimako ga mutanen kasar.
Asusun ya sanar da wannan tallafin kudi bayan kungiyoyin agajin sun bayyana bukatarsu ta dalar Amurka biliyan 1,81 a shekarar 2015 domin ba da taimako ga mutane miliyan 4,1 dake cikin bukata sosai. (Maman Ada)