in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da korar wakilinta daga Sudan ta Kudu
2015-06-02 10:11:45 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah wadai da korar mataimakinsa na musamman mai kula da ayyukan majalissar a Sudan ta Kudu da mahukuntan kasar suka yi, yana mai kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta sauya wannan matsaya.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya ce, Toby Lanzer, wanda hukumomin Sudan ta Kudun suka umarta da ficewa daga kasar, yana taka muhimmiyar rawa, wajen cimma nasarar ayyukan jin kai, musamman ga al'ummun kasar, wadanda tashe-tashen hankula suka fi shafa.

Sanarwar ta kara da cewa, da zarar wa'adin aikin Mr. Lanzer ya kammala, Mr Eugene Owusu daga kasar Ghana zai maye gurbinsa.

An nada Lanzer dan asalin kasar Birtaniya a matsayin mataimaki na musamman ga babban magatakardar MDD a Sudan ta Kudu ne cikin shekarar 2012. Ana kuma sa ran zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukan majalissar da suka shafi yankunan Sahel.

Mahukuntan Sudan ta Kudu dai ba su bayyana wani dalili na korar jami'in ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China