Ya ce, a kokarin sa kaimi ga gudanar da shirin "Ziri daya da hanya daya" tare da cimma babbar nasara, dole ne a sa kaimi ga gudanar da wasu muhimman ayyukan hadin gwiwa.
Kuma Ou ya ce, a yayin da ake kokarin sa kaimi ga ayyukan hadin gwiwa, dole ne a dora muhimmanci kan yin mu'amala wajen kafa manyan ayyukan amfanin jama'a, da yin hadin gwiwa a fannonin masana'antu da makamashi, sabo da zurfafa hadin gwiwa a fannin masana'antu zai biya bukatun kasashen dake zirin ko dake hanya, tare da kyautata tsarin masana'antun Sin. Shi ya sa, hakan zai kasance muhimmiyar hanya wajen sa kaimi ga yininganta hadin gwiwa tsakaninsu da Sin a fannin tattalin arziki.(fatima)