Taron matsan shugabannin Sin da Afrika karo na 3 da aka kammala a ranar Lahadin nan ya yi kira ga kasashen Afrika da su yi nasu tsarin da zai taimaka musu wajen habaka tattalin arzikin nahiyar wanda shi ne wani bangare babba da zai inganta zamantakewar al'umma.
Da yake rufe taron, mataimakin shugaban kasar Tanzaniya Mohammed Gharib Bilal ya jaddada bukatar da masu ruwa da tsaki su tsara abubuwan da za su kawo zuba jari sosai a nahiyar, yana mai cewa, a lokacin da ake duba yiwuwar hakan, a fili yake cewa ba za'a iya kaucewa sabbin ci gaban zamani dake kunno kai ba.
A cewar Mr. Bilal, abu mafi muhimmanci shi ne Afrika ta yi nata tsarin wanda zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin tasu samun tsayawa da kafafunsu. Ya kara da cewa, ana ta gano albarkatun kasa da dama a sassa daban daban na nahiyar kamar mai, iskar gas, sinadarin uranium, duwatsu masu daraja, kamar su zinarai, lu'u lu'u, da sauran karafa, amma a wassu kasashen hakan ya zama masifa maimakon alheri saboda al'ummarsu a ciki da waje suna fada a kan wannan albarkatun kasa a ko da yaushe.
Mataimakin shugaban kasar na Tanzaniya daga nan sai ya ce, dole ne Afrika ta rike matsayinta a kula da tattalin arzikinta, muddin za ta iya saka amincewa da juna a tsakani, a nan mulki mai kyau da iya sa ido yadda ya kamata, rashin rufa rufa a komai, yaki da cin hanci da rashawa, da doka na gari dole ne a bi su a ko wane hali. (Fatimah)