Wani rahoton bincike da bankin duniya ya fitar ya nuna cewa, talauci a Najeriya ya ragu daga kaso 35.2 bisa dari, ya zuwa kaso 33.1 bisa dari a shekarar 2013 da ta gabata.
Wannan sakamako, a cewar rahoton, ya sauya matsayin tsanantar hauhawar talauci a kasar, wanda a tsakanin shekarun 2009 zuwa 2010, ya kai ga kaso 62.2 bisa dari bisa mizanin kididdiga na HNLSS.
Da yake karin haske game da hakan, mukaddashin shugaban bankin na duniya reshen Najeriya John Litwack, ya ce, kaso 33.1 da aka samu na wakiltar matsakaicin kason binciken da bankin ya gudanar ne a tsakanin shekarun 2012 zuwa da 2013. Inda a kauyuka, ake da kaso 44.9 bisa dari, sabanin birane da ke da kaso 12.6 bisa dari.
Kaza lika jami'in na bankin duniya ya ce, alkaluma sun nuna talauci ya fi kamari ne a yankunan arewa idan an kwatanta da kudancin kasar, yayin da a hannu gida, adadin 'yan najeriyar dake cikin kangin talauci, ya kai mutane miliyan 58, wadanda rabin su ke zaune a sassan arewa maso gabashi, da arewa maso yammacin kasar. (Saminu)