Gwamnatin tarayyar Nigeriya ta ce, ta fara kokarin daidaita fagen kasuwanninta don hana wasu ikon rike wannan bangaren su kadai, a wani yunkuri na samar da yanayi mai kyau da kuma gasa bisa adalci a masana'antu, bangaren kasuwanci da zuba jari.
A dangane da haka, za'a fara wani shiri na ba da sararin yin gasa mai tsabta da kariya ga 'yan kasuwa, wadanda masu sayen kaya za su gamsu, musamman ta bangaren tattalin arziki.
Ministan masana'antu, ciniki da zuba jari na kasar Olusegun Aganga wanda ya sanar da hakan a ranar Alhamis din nan a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeriya, ya yi bayanin cewa, wannan sabon tsarin zai kawo karshen salo mai da nau'in kasuwanci na bangare mai zaman kan shi ko kungiya, ya samar da gasa mai tsabta a ciniki da masu sayen kayan za su more, abin da suka saya da kudinsu.
Mr. Aganga ya bayyana hakan ne a wani dandalin mika rahoton sharen fage a kan gasa da tsarin ba da kariya ga masu sayayya ga ma'aikatu, manyan hukumomi na musamman, kungiyoyin 'yan kasuwa, da kuma jihohin arewacin kasar.
Ministan wanda babban sakataren ma'aikatar jakada Abdulkadir Musa ya wakilta ya ce, dangane da sabon shirin kwaskwarima na kasar da shugaba Goodluck Jonathan yake aiwatarwa, da kuma gyare-gyare da ake yi a wassu manyan bangarori na tattalin arzikin Nigeriya, gwamnatin tarayya ta ga ya zama wajibi a gaggauta samun daidaito a tsarinta da sauran kasashen duniya domin bin doka da tsari na shugabantar ba da kariya ga masu ciniki da kuma ingiza gyaran da ake yi a wannan bangaren. (Fatimah)