Bankin duniya ya amince da bai wa kasar Najeriya rancen kudi na dalar Amurka miliyan 250, domin kyautata ingancin tsarin samar da ruwan sha a cikin wannan kasa dake yammacin Afrika, in ji kakakin bankin a ranar Talata.
Bamidele Oladokun, wani kakakin shiyyar Afrika na bankin duniya ya bayyana cewa, bashin kudin da hukumarsa ta amince zai taimaka ainun ga kyautata ingancin tsarin samar da ruwa na yanzu a kasar Najeriya.
Shirin na neman bullo da wasu nagartatttun hanyoyi ga talakawa da su cigaba da gudanar da harkokinsu na ilimantarwa da kuma samun alfanu, in ji wannan jami'i.
Haka zai baiwa talakawa damar taimakawa junansu domin fita daga kangin talauci, maimakon bata lokaci wajen jan ruwa rijiya, in ji mista Oladokun a cikin wata sanarwa a birnin Abuja.
Haka kuma jami'in ya cigaba da cewa, wadannan kudade za su taimakawa kimanin mutane miliyan biyu a Najeriya, musammun ma mazauna birane dake fama da rashin jari a cikin manyan biranen jahohi da kuma biranen dake kewayensu. (Maman Ada)