Tarayyar Najeriya ta yi alkawarin ba da dalar Amurka miliyan hamsin domin tabbatar da shirin gina babbar hanyar Abidjan-Lagos, da aka tsai da a cikin watan Mayun shekarar 2013 a yayin babban taron kungiyar tarayyar Afrika AU da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, in ji ministan gine-ginen Najeriya, mista Mike Oziegbe Onolememen a ranar Litinin a birnin Cotonou na kasar Benin a yayin bude taron kwamitin kula da shirin gina wannan hanyar da za ta ratsa Abidjan zuwa Lagos.
A nasa bangare, ministan gine-gine da sufuri na kasar Benin, Natonde Ake, ya bayyana cewa, wannan shirin wani muhimmin abu ne domin cigaban tattalin arziki da zaman al'umma ga shiyyar yammacin Afrika.
Wannan shirin gina hanya wani aiki ne da za'a kara yin musanya a kan wannan babbar hanyan da za ta ratsa manyan biranen yammacin Afrika, in ji mista Ake. (Maman Ada)