Rahoton ya bayyana cewa, alkaluman tattalin arzikin kasashe 5 na nahiyar Asiya wato Sin, Indiya, Koriya ta Kudu, Japan da kuma Indonesia ya ragu a kai a kai a cikin watanni biyar da suka gabata, wannan ya nuna cewa, bunkasuwar tattalin arzikinsu ta fuskanci tafiyar hawainiya.
Tun daga karshen shekarar 2013, har zuwa yanzu, cikakken alkaluman tattalin arziki ta kasashe mambobin OECD ta kiyaye 100.6, wannan ya bayyana cewa, an kiyaye karfin raya tattalin arziki a kasashen. (Zainab)