Maimakon karuwar tattalin arziki, an fi mai da hankali kan hanyoyin da suka dace na samun karuwar tattalin arziki a taron na wannan karo. Shugabar kula da harkokin Afirka na taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya Elsie Kanza ce ta bayyana haka kafin a fara taron. Ta kuma kara da cewa, babban makasudin taron shi ne ciyar da hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka gaba da kuma kawar da nuna bambanci, don samun dauwamammen ci gaba na tattalin arzikin a kasashen Afirka.
Bugu da kari, firaministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke yin ziyarar aiki a Nijeriya zai halarci wannan taro, inda zai ba da wami muhimmin jawabi kan karfafa hadin gwiwar dake tsakannin kasar Sin da kasashen Afirka, ciyar da aikin bunkasuwar kasashen Afirka gaba, da kuma cimma burin bunkasa Sin da Afirka cikin hadin gwiwa. (Maryam)