Ranar 17 ga wata, rana ce ta sadarwa da sakonni ta duniya, domin wannan rana ta musamman, babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-Moon ya ba da jawabi a ranar Jumma'a 16 ga wata kan wannan batu, inda ya yi kira da a yi kokarin samun samu bunkasuwa mai dorewa yayin da akebisa amfani da kimiyyar fasahar sadarwa ta zamani.
A cikin jawabin nasa, Mr Ban ya ce, kimiyyar fasahar sadarwa wani karfi ne na tushe wajen wanda ke tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wadda wanda kuma ke samar da dabaru iri daban-daban wajen samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa da wadatar duniya baki daya.
Ban da haka, mista Ban ya ce yYanar gizo ta Intanet ta zama mataki mai yakini muhimmanci wajen yin kwaskwarima kan samun bunkasuwar tattalin arziki da al'umma baki daya ba tare da gurbata muhalli ba, wanda ya kasance babban ginshiki wajen samun bunkasuwa mai dorewa. Kuma ya kasance babban aiki da za a maida hankali wajen domin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015. (Amina)