in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka ba sa iya dorewa wajen bin tafarkin raya tattalin arziki, in ji wani rahoto
2014-05-20 15:18:57 cri

Cibiyar nazarin sauyin tsarin tattalin arzikin nahiyar Afirka, ta gabatar da wani rahoto a ranar 19 ga wata a birnin Kigali, helkwatar kasar Ruwanda.

Rahoton dai ya bayyana cewa, ko da yake a halin yanzu wasu kasashen Afirka sun samu bunkasuwa a fannin tattalin arziki, amma kasashen ba sa dorewa a hanyar da suke bi na raya tattalin arzikinsu. Rahoton dai na nuni da cewa hanyar da kasashen na Afirka ke bi yanzu haka, ba za ta haifar musu da kyautatuwar tattalin arziki, da bunkasuwa cikin dogon lokaci ba.

Rahoton ya kimanta ma'aunin sauyawar tattalin arzikin kasashen Afirka 21 da ke kudu da Sahara, inda ya yi nuni da cewa, kasashe uku dake kan gaba a wannan fanni, su ne Mauritius, da Afirka ta Kudu, da kuma Kodebuwa. Rahoton ya kuma gano cewa yawancin kasashen Afirka, su na dogaro ne kan ma'adanai da man fetur, wadanda ba sa samarwa matasan su isassun ayyukan yi.

Har ila yau wasu manyan kasashen Afirka na samun koma baya a fannin tattalin arziki, matakin da mai yiyuwa ya kai ga haifar da rashin karko a tsarin siyasa, da zamantakewar al'umma.

Shugaban cibiyar Dr. Kengsley Amoako ya ce, a halin yanzu kasashen Afirka suna bukatar samun bunkasuwa ta fannoni daban daban, ciki har da inganta karfin takara wajen fitar da kaya zuwa ketare, da kwarewa a fannin samar da kayayyaki, da kirkire-kirkire a fannonin fasahohi, ta yadda za su iya samun hakikanin sauyi ga bunkasuwar su. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China