in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bokon Haram ta kashe mutane 32 kan iyakar Najeriya da Kamaru
2014-05-30 09:28:26 cri

Aka kashe a kalla mutane 32 a ranar Alhamis a yayin wasu 'yan tada kayar baya suka kai hari a wani kauyen dake kusa kan iyakar Kamaru da Najeriya a cikin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, a cewar wata majiya jami'an tsoro dake zargin kungiyar Boko Haram da aikata wannan danyen aiki.

Wani hafsan soja, da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, bisa yadda mutane masu dauke da makamai suka kai wannan hari, yana kama da na Boko Haram, kungiyar dake kawo barazana sosai ga tsaron kasar Najeriya tun daga bakin shekarar 2009.

A cewar majiyar, wadanda suka tsira da rayukansu a yayin harin kauyen Gurmushi na cigaba da kidayar asarar da suka samu, domin maharani sun kuma lalata dukiyoyi da gida. A kalla mutane 32 suka mutu, dukkansu fararen hula ne, in ji wannan majiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China