Rundunar tsaron kasar Kamaru, ta gano wani sansanin 'ya'yan kungiyar nan ta Boko Haram shake da makamai, a wani wuri dake kusa da iyakar kasar da Chadi.
Helkwatar rundunar sojin Najeriya ce dai ta tabbatar da hakan, cikin wata sanarwa da kakakinta Chris Olukolade ya sanyawa hannu. Sanarwar ta kara da cewa, hadin gwiwar da kasashe makwaftan Najeriya ke yi, ya fara haifar da nasarar da ake fata.
Makaman da aka samu a sansanin na 'yan Boko Haram, sun hada da manya da kananan bindigogi, da rokoki, da harsasai, da kuma bamabamai kirar hannu. Sanarwar ta kara da cewa, wannan nasara ta biyo bayan cafke wasu masu safarar makamai ga kungiyar ne su biyu, da jami'an tsaro suka yi a kwanan baya a Najeriya.
Haka zalika an samu wasu fasfunan kasar Kamaru sama da 50, da wata mota kirar Jeep. Kakakin rundunar sojin Najeriyar, ya kuma ce, ana ci gaba da cafke makamai nau'o'i daban daban, sakamakon bayanan da aka samu daga wasu 'yan kungiyar da aka cafke a baya bayan nan. (Saminu)