An kashe a kalla jami'an tsaro 24 a wani rikici da wasu mayaka da ake zargi 'yan Boko Haram ne a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria.
Wata majiyar sojoji a Nigeria ta ce, al'ummar Buni Yadi dake yankin karamar hukumar Gujba ta jihar dake arewacin Nigeria ta ce, a kan idon 'yan garin na Buni Yadi ne, wasu mayaka suka kai hari a sansanin 'yan sanda masu sintiri da sojoji wadanda ke bakin aikinsu, hakan ya haddasa musayar wuta.
Kamar yadda majiyar ta ce, an ga gawawwakin 'yan sanda 14 da sojoji 10 warwatse a yankin, a ranar Talata, bayan harbe-harben da aka yi awowi ana yi.
Majiyar ta kara da cewar, an garzaya asibitin babban birnin jihar ta Yobe Damaturu, da wasu jami'an tsaro da suka samu rauni.
Buni Yadi, wanda ke kudancin Yobe ya fuskanci mummunan hari a watan Fabarairun da ya gabata, lokacin da mayakan Boko Haram suka dauki alhakin kashe yaran makaranta 49. (Suwaiba)