in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararrun tsaro za su isa Najeriya domin sa ido kan barazanar Boko Haram
2014-05-22 10:58:21 cri

Bayan wani zaman taro da aka shirya daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Mayu a birnin Ouagadougou na kasar Burkina-Faso kan matsalar tsaro a yankin Sahel dake fama da karuwar miyagun laifuffukan kasa da kasa da ma wasu ayyukan ta'addanci, shugabannin hukumomin leken asiri sun cimma yarjejeniyar tura a karkashin kungiyar tarayyar Afrika AU wata tawagar kwararru a Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Bisa yadda ya kamata a tabbatar da aiki, da kuma karfafa kokarin da ake, mahalarta taron karo na biyar na shugabannin hukumomin leken asiri na kasashen yankin Sahel sun dauki niyyar tura wata tawagar kwararru a fannin tsaro a Najeriya domin yin musanyar bayanai da kwarewa tare da manyan jami'an Najeriya kan kokarin yaki da kungiyar Boko Haram, in ji sanarwar karshen taron.

A watan da ya gabata, kungiyar Boko Haram ta sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a arewa maso gabashin Najeriya, tare da barazanar da sayar da su ko auratar da su da karfi.

A ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2014, wasu tagwayen hare-hare da ake zargin mayakan Boko Haram da aikata sun hallaka mutane a kalla 118, tare da jikkata 56 a wata kasuwar birnin Jos dake tsakiyar Najeriya.

Ina fatan za'a mai da hankali sosai domin binciken barazanar ta'addanci da kungiyar Boko Haram take janyo wa, da bullo da nagartattun matakan da ya kamata a dauka na gaggawa domin tallafawa kokarin jami'an tsaron Najeriya, in ji kwamishinan zaman lafiya da tsaro na tarayyar Afrika, Smail Schergui a yayin taron na Ouagadougou, tare da jaddada allawadan kungiyar AU kan ayyukan Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China