'Yan sandan kasar sun bayyana cewa, canja hanyar da jirgin ruwan ya yi cikin gaggawa ce ta haddasa motsawar kayayyakin dake cikinsa, wanda kuma hakan ya sanya shi kifewa ya kuma nutse nan take.
A safiyar Alhamis din nan kuma 'yan sandan ruwan yankin sun ci gaba da aikin ceton da suke yi, duk da yanayin gudun ruwan, da kuma karancin haske a karkashinsa dake yiwa aiki tarnaki. (Maryam)