in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugabar kasar Koriya ta Kudu
2013-06-29 16:48:25 cri
Firaministan kasar Sin, Mista Li Keqiang, a ranar Jumma'a 28 ga wata a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya gana da Madam Park Guen-hye, shugabar kasar Koriya ta Kudu, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka hada da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2, aikin gina yankin ciniki cikin 'yanci, maganar makaman nukiliya a zirin Koriya, da dai makamantansu.

A wajen ganawar tasu, firaminista Li Keqiang ya ce, Sin da Koriya ta Kudu sun kasance makwabta, kuma abokan dake hada kai a wasu muhimman fannoni, don haka ya kamata kasashen 2 su yi hangen nesa da kokarin samun ci gaba, don zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, zuba jari, hada-hadar kudi, sabbin makamashi, da dai sauransu, da kara azama ga aikin gina yankin ciniki mai 'yanci, ta yadda jama'ar kasashen 2 zasu ci moriya.

A cewar Mista Li, kasar Sin tana kokarin raya masana'antu, da gina karin garuruwa, don haka ta kasance wata babbar kasuwa dake da bukatu matuka. Sa'an nan kasar tana kokarin sanya tattalin arziki ya zauna da gindinsa, gami da neman damar ciyar da shi gaba, wadanda ayyuka ne da za su samar da dama sosai ga hadin gwiwar kasashen Sin da Koriya ta Kudu.

Don haka, Mista Li ya bayyana fatansa na ganin bangarorin 2 zasu yi amfani da fannonin da za su iya taimakawa juna, kamarsu fasahohi, kasuwanni, da kwararru, don zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu. Wannan lamarin a ganinsa zai amfana kasashen 2, da taimakawa ci gaban tattalin arzikin yankin da kasashen 2 suke ciki, kana zai habbaka hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen dake yankin gabashin Asiya.

Yayin da ya yi magana kan yanayin da ake ciki a zirin Koriya, firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya ce, kasar Sin ta dade tana tsayawa kan ganin an kau da makaman nukiliya daga zirin Koriya, ra'ayin da ta bayyana shi a fili, wanda ba zai canza ba. Dalilin da ya sa haka shi ne domin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan ganin a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya. Kana kasar na son yi kokari tare da sauran bangarorin kasa da kasa, don daidaita wannan matsala ta hanyar shawarwari.

A nata bangare, Madam Park Guen-hye, ta bayyana cewa, ita da shugabannin kasar Sin sun cimma ra'ayi daya kan hanyar da za a bi don raya huldar dake tsakanin Koriya ta Kudu da kasar Sin a nan gaba, wanda ya kasance babban sakamakon da ta samu bisa ziyararta zuwa kasar Sin. A cewar Madam Park, dukkan kasashen 2 na fuskantar ayyukan raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, don haka Koriya ta Kudu na son zurfafa hadin kan bangarorin 2 a fannoni daban daban, da kara zuba jari a yammaci da tsakiyar kasar Sin, da neman kulla yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tsakanin bangarorin 2 tun da wuri, ta yadda za a samu damar zurfafa hadin gwiwar kasashen 2 don moriyar jama'arsu da na yankin da suke ciki gaba daya. Haka zalika, kasar Koriya ta Kudu ta yaba ma kasar Sin kan kokarinta na neman daidaita matsalolin da ake fuskanta a zirin Koriya, kana kasar na son ci gaba da kokarin mu'amala tare da kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China