in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta rike matsayinta na 38 a jadawalin hukumar FIFA
2014-05-14 16:33:10 cri
Wani sabon jadawali na kwarewar kulaflikan kwallon kafa da hukumar FIFA ta fitar a ranar Alhamis din data gabata, ya nuna cewa kulaf din Black Stars na kasar Ghana na ci gaba da rike matsayin sa na 38, a jerin kulaflikan kasashen duniya. Kaza lika Black Stars din shi ne na 4 a daukacin nahiyar Afirka da maki 713 bisa ma'aunin hukumar ta FIFA.

Har wa yau bisa jadawalin na FIFA, kulaf din kasar Cote d'Ivoire ne na daya a nahiyar ta Afirka, sai kuma Masar dake biye a matsayi na 2 yayin da kuma Algeria ke a matsayi na 3.

Game da kulaflikan kasashen duniya dake kan gaba a wancan jadawali kuwa, kasar Sifaniya ce ke ci gaba da rike kambin ta a matsayi na daya, za kuma ta kara a rukuni guda tare da Ghana, a gasar cin kofin duniya dake tafe. A matsayi na biyu kuwa kulaf din kasar Jamus ne ke biyewa Sifaniya, yayin da kuma kulaf din kasar Portugal ke matsayi na 3.

Bugu da kari hukumar ta FIFA ta ce, a kalla kulaflikan kasashe 143 ne suka rike matsayin da suke kai a watan Afirilu, a sabuwar kididdigar da ta fitar a wannan wata na Mayu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China