in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin nasarar Roma ya karawa Juventus damar rike kambin Serie A
2014-05-06 15:39:39 cri
A fagen gasar Serie A ta kasar Italiya, yadda kulob din Catania ya lashe kulob din Roma da ci 4 da 1 a ranar Lahadi 4 ga wata ya baiwa 'yan kallo mamaki kwarai, kana wannan shan kayen da Roma ta fuskanta ya zama tamkar mika kambin Serie A ne, na wannan kakar wasanni ga takwaransa na Juventus.

Lashe Roma a wannan lokaci da ake daf da kammala wasannin gasa ta bana, ya tabbatar da cewa Roman wadda ita ce ke biyewa Juvenstus a teburin gasar a matsayi na biyu karkashin babban kocinsa Rudi Garcia, ba za ta iya cike gibin maki 8 dake tsakanin ta da Juventus din ba.

A wasan da aka buga a ranar Lahadi da ta gabata, Mariano Izco na kungiyar Catania shi ne ya jefa kwallaye 2 cikin ragar Roma, kafin Francesco Totti ya farkewa Roman kwallo daya. Amma bayan hutun rabin lokaci Gonzalo Bergessio da Pablo Barrientos sun samu nasarar kara yawan kwallayen da aka ci Roman a wannan wasa, aka kuma tashi Catania na da kwallo hudu Roma na da daya.

Wannan nasara da Catania ta samu kan Roma ya sanya ta dagawa sama a teburin gasa, duk da cewa har yanzu tana wani matsayi na koma baya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China