in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Schalke ya sabunta yarjejeniyar Ralf Faehrmann
2014-05-06 15:40:20 cri
Kulaf din Schalke da ke buga gasar Bundesliga ta kasar Jamus, ya sanar da tsawaita wa'adin yarjejeniyar da ya kulla da mai tsaron gidansa Ralf Faehrmann ya zuwa watan Yunin shekarar 2019.

Kulob din ya ba Faehrmann karin wa'adi na shekaru 4, a matsayin wata kyautar yabo kan yadda ya nuna cikakken kwazonsa, da kwarewa a kakar wasannin da ake ciki, matakin da ya taimakawa kulob din samun tikitin halartar gasar zakarun turai a kaka mai zuwa.

Darektan kulob din na Schalke Horst Heldt, wanda ya bayyana hakan a madadin kungiyar, ya kuma yabawa Faehrmann kwarai bisa kokarinsa, inda ya ce duk da cewa mai tsaron gidan ya sha fama da jinya a wannan kakar wasanni, a hannu guda ya yi kokarin samun horo, ya kuma koma filin wasa ba tare da wani bata lokaci ba. Ya ce dan wasan ya taka muhimmiyar rawa musamman ma a rabin kakar wasannin ta karshe.

Ralf Faehrmann mai shekaru 25 a duniya, wanda ya tsare gidan Schalke a wasanni 50 da kulaf din ya buga, shi ma ya nuna farin cikinsa bisa ci gaba da kasancewar sa a wannan kulaf na Schalke. Kulaf din da yanzu haka ke matsayi na 3, a teburin gasar Bundesliga, ya kuma dara Leverkusen dake matsayi na 4 da maki 3.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China