in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rio de Janeiro ta gabatar da shiri domin gasar cin kofin duniya
2014-05-06 15:38:50 cri
Magajin birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, Eduardo Paes, ya kaddamar da wani shirin musamman, game da yadda za a tafiyar da harkokin birnin ta fuskar zirga-zirga, a daidai wannan lokaci da ake share fagen fara gasar cin kofin duniya, wadda za a kwashe wata guda ana gudanarwa daga ranar 12 ga watan Yuni mai zuwa.

Birnin Rio, a matsayin daya daga cikin biranen kasar Brazil 12 da za su karbi bakuncin wasannin gasar, zai karbi bakuncin wasanni 7, ciki har da wasan karshe da zai gudana a ranar 13 ga watan Yuli a shahararren filin wasa na Maracana, wanda aka masa kwaskwarima sosai don dacewa da bukatar hukumar FIFA.

Haka zalika, birnin Rio zai kasance wurin da za a kafa cibiyar manema labaru, da ofishin hukumar FIFA, a lokacin gasar cin kofin na duniya.

Wannan shirin da magajin Rio ya gabatar ya nuna tsarin da za a bi wajen gudanar da ayyukan birnin a fannoni daban daban, yayin gasar cin kofin duniya ke gudanarwa. Misali akwai aikin da ya shafi zirga-zirgar jama'a, wanda bisa la'akari da 'yan yawon shakatawa da yawansu zai kai dubu 600 da gasar cin kofin duniya za ta janyo wa birnin, ya sa hukumar birnin ta sanar da hutun kwanaki 3 a yayin wasannin da za su gudana a filin wasan Maracana, ta hakan ana sa ran ganin yawan motocin dake zirga-zirga kan hanya sun ragu.

Hukumar birnin Rio na fatan ganin mafi yawan 'yan yawon shakatawa za su yi amfani da layukan jirgin kasa na cikin gari, don zuwa filayen wasa, kana ana sa ran ganin wani tsari na motocin bas masu sauri, wanda aka kafa musamman ma domin gasar cin kofin na duniya, wanda shi ma zai fara aiki a lokacin gasar.

Ko da yake yanzu aikin gina tsarin bas din ya samu jinkiri sosai, wanda zai hana kaddamar da dukkan tashohin bas din, amma ana sa ran ganin a kalla wani layin motocin bas mai muhimmanci da ya hada filin saukar jiragen sama, da ungwannin dake dab da teku, inda aka fi samun otel-otel masu kyau, zai fara aiki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China