Tuni dai kasashen Amurka da Rasha suka nuna damuwarsu don gane da halin zaman dar dar da ake ciki a wannan ziri na Koriya.
Da yake tsoakaci kan wannan batu, kakakin fadar Amurka ta White House Jay Carney ya ce, atisayen da kasar Koriya ta Arewa ke gudanarwa a 'yan kwanakin nan na da matukar hadari ne, kuma yana iya haifar da tashin hankali ga kasar Koriya ta Kudu. Ya ce, Amurka na jaddada alkawarin kiyaye tsaron kasashen da take kawance da su.
A nata bangare, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar ta shafin yanar gizonta cewa, kasarta tana damuwa kwarai da yanayin makurdadar Koriya, inda ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da daukar matakan da za su iya haddasa karin rikici a yankin. (Maryam)