Kang Byung–Kyu,Ministan tsaro da harkokin mulki na kasar ya shaida ma manema labarai cewa an ceto mutane 164, daga cikin su akwai daliban makarantar gaba da firamare 78 sannan kuma an tabbatar da mutuwar Karin mutun daya abinda ya kai adadin wadanda suka mutu zuwa 3 da suka hada da ma'aikaciyar jirgin mace daya 'yar shekaru 22 da kuma wassu maza biyu daliban makarantar gaba da firamare.
A cewar ma'aikatar akwai mutane 292 da har yanzu sun bace a cikin tekun sai dai akwai fargaban adadin zai karu zuwa 295 kamar yadda masu tsaron bakin ruwan suka tabbatar cewa wadanda ke cikin jirgin su 462 maimakon 459 da ma'aikatar ta sanar tun da farko.(Fatimah Jibril)