Kwamitin tsaron MDD, ya amince da kudurin tsawaita wa'adin aikin kwamitin kwararru, mai sanya ido ga aiwatar da dokar hana yaduwar makamai, da dakile ayyukan masu barazana ga dorewar yanayin zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan.
An cimma kudurin tsawaita wa'adin aikin kwamitin da watanni 13 ne, yayin zaman kwamitin na ranar Alhamis, bayan da aka yi imanin cewa, halin da ake ciki a wasu yankunan kasar ta Sudan na zamantowa barazana ga kyautatuwar yanayin tsaron kasa da kasa.
Kafin tabbatar da wannan kuduri, sai da mambobin kwamitin tsaron suka hakkake cewa, ba za a iya shawo kan matsalolin siyasar dake addabar yankin na Darfur ta hanyar amfani da karfin tuwo ba.
Har ila yau kwamitin ya jaddada bukatar tashi tsaye, wajen ganin an kawo karshen tashe-tashen hankula, da karancin tsaro dake barazana ga rayukan fararen hular dake zaune a yankin na Darfur cikin 'yan watannin nan.
Bugu da kari, kwamitin tsaron ya ja hankalin mahukuntan kasar ta Sudan, da su yi hadin gwiwa da ragowar masu ruwa da tsaki, wajen tabbatar da daukar matakan warware matsalolin da ake fuskanta, domin ba da kariya ga rayukan fararen hula. (Saminu)