Jagoran tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD da ke Darfur kana mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan samar da zaman lafiya Herve Ladsous, ya bayyana cewa, yanayin tsaro ya tabarbare a Darfur a shekarar 2013, kuma har yanzu ana fuskantar tashin hankali.
Mr. Ladsous ya bayyana hakan ne yayin da yake yiwa kwamitin sulhu bayani game da yanayin da ake ciki a Darfur, inda ya ce, a 'yan kwanakin nan, al'amuran jin kai sun kara rincabewa, sannan ana ci gaba da kaiwa ma'aikatan MDD hari, inda a shekara ta 2013, aka kashe ma'aikatanta wanzar da zaman lafiya 16.
Don haka, ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke Darfur, da su shiga shirin sulhuntawa da nufin tsagaita bude baki daya tare da samar da zaman lafiya ga mutanen da ke zaune a yankunan da ake gwabza fada na Sudan.
Jami'in na MDD ya ce, yanzu yarjejeniyar Doha da aka cimma game da samar da zaman lafiya a Darfur tana tafiyar hawainiya, inda sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar, bisa martaba ta sosai, abin da ya sa al'ummomin da ke zaune a yankin na Darfur ba su amfana da ita sosai ba.
Ya zuwa yanzu, gwamnatin Sudan da manyan kungiyoyin 'yan tawaye, wato LJM da JEM suna martaba yarjejeniyar, sai dai akwai bukatar su kara mutunta dukkan muhimman abubuwan da aka daddale.
Bayanai na nuna cewa, yawan mutanen da suka bar gidajensu ya karu zuwa kimanin miliyan 2, inda aka kiyasta cewa, an tilastawa mutane 400,000 yin kaura sakamakon sabon fadan da ya barke a shekarar da ta gabata. Yayin da mutane kusan 300,000 suka mutu, tun lokacin da fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan tawaye da dakarun gwamnati da kawayensu.
A halin yanzu kusan mutane miliyan 3.5 kwatankwacin kashi 30 cikin 100 na yawan al'ummar Darfur na samun tallafin jin kai ne daga al'ummomin kasa da kasa. (Ibrahim)