Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a jiya Lahadi ya ce, ya kadu matuka game da wani sabon harin da wadansu masu dauke da makamai suka kai a kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Darfur, yana mai kira ga gwamnatin kasar Sudan da ta gurfanar da wadanda suka yi wannan aika a gaban shari'a.
Kamar yadda wata sanarwa ta bakin kakakinsa ta yi bayani, an ce, wadansu mutane masu dauke da makamai da ba'a san ko su wanene ba a jiya Lahadi 29 ga wata suka kai hari a kan tawagar ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwwa tsakanin MDD da kungiyar tarayyar kasashen AU UNAMID a kusa da garin Greida dake kudancin Darfur, inda nan take aka kashe ma'aikata biyu, 'dan asalin kasar Jordan da kuma 'dan asalin kasar Senegal.
Wannan hari na baya bayan nan ya kawo adadin ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na UNAMID wadanda aka kashe zuwa 16 a cikin wannan shekara bisa kididdigar majalissar bayan harin da aka kai wa ma'aikatan a watan jiya da ya hallaka 'dan asalin kasar Ruwanda guda daya a arewacin Darfur.
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kafa wannan ofishin hadin gwiwwar UNMID a shekara ta 2007, da zummar ba da kariya ga fararen hula da kuma samar da tsaro ga kayayyakin agaji a Darfur, inda fada tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawaye ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300,000, tare da sanadiyyar rasa matsugunnen mazaune sama da miliyan 2 a cikin shekaru 10 da ake ta gwabza fada. (Fatimah)