Kakakin MDD Martin Nesirky, ya shaidawa manema labarai ranar Litinin cewa, tawagar MDD da ke aiki a yankin Darfur na kasar Sudan (UNAMID), ta bayyana damuwa matuka game da fadace-fadacen kabilanci na baya-bayan nan da ya faru a yankin.
Ya ce, tawagar ta UNAMID ta damu sosai game da tashin hankalin da ke faruwa a wasu wuraren yankin Darfur a cikin 'yan makonnin nan, inda tawagar ta samu rahotannin barkewar fadan kabilanci tsakanin al'ummun Misseriya, Taisha da Salamat a wurare daban-daban da ke yankin kudu maso yammacin tsakiyar Darfur a kwanakin da suka gabata, kuma tawagar tana kokarin tantance irin asarar da aka tabka, ciki har da yawan wadanda suka jikkata.
A cewar kakakin na MDD, bugu da kari, tawagar ta UNAMID ta bayar da rahoto a ranar Litinin cewa, wani kwamiti mai kunshe da shugabanni da wakilan kabilun daban-daban, sun gana a tsakiyar Darfur da nufin cimma yarjejeniyar zaman lafiya kan fadan na baya-bayan.
Rahotannin farko na bayyana cewa, mayakan kabilun sun yi amfani da rokoki, makaman atilari da manyan bindigogi a fadan da suka yi na ranar Lahadi a yankin kudu maso yammacin yankin na Darfur. (Ibrahim)