Har wa yau kuma, shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya ce, Dr. Goodluck Jonathan zai kai ziyara kasar Afirka ta Kudu a wata mai zuwa, inda za su ci gaba da zurfafa shawarwari a kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi nahiyar Afirka.
A waje daya kuma, mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak ya ce, ziyarar Jacob Zuma a Najeriya na da muhimmanci kwarai da gaske.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.