Fashola ya bayyana cewa, aikin raya yankin yin cinikayya cikin sauki na Lekki zai kara samar da guraben aikin yi ga 'yan Nijeriya, kawo Karin arziki ga kasar, kana zai sa kaimi ga raya masana'antun kasar Nijeriya. Hakazalika, zai yi amfani wajen raya tattalin arzikin kasar na dogon lokaci.
Babban manajan kamfanin raya yankin cinikayya na Lekki Chen Xiaoxing ya bayyana cewa, Nijeriya na da al'umma mafi yawa a nahiyar Afrika, wato kenan tana da babbar kasuwa.
Bayan da tattalin arzikin Nijeriya ya habaka, za a shiga cikin yunkurin raya masana'antun kasar, sannan jama'a za su yi tururuwa zuwa birane don neman dammar samun aikin yi.
Yankin yin cinikayya cikin sauki na Lekki ya samar da wani dandali na saka jari, wanda zai baiwa masu saka jari da suka zo daga duk duniya damar bude sana'o'insu a Nijeriya, da kuma sa kaimi ga raya tattalin arzikin Nijeriya, gami da samar da guraben aikin yi a wurin.
Yankin yin cinikayya cikin sauki na hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya mai suna Lekki yana zirin Lekki da ke kasar Nijeriya, yana da nisan kilomita 50 daga cikin birnin Lagos,kuma kamfanin Lekki na jarin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika, da kuma gwamnatin jihar Lagos ne suka hada hannu tare, don gina shi.(Bako)