A jiya Alhamis 3 ga wata, kamfanin jirgin saman Dana na kasar Nijeriya ya dawo da zirga-zirga a lokacin da ya kwashi fasinjojin farko daga Ikko zuwa Abuja watannin 7 da faduwarsa.
Jirgin da ya fara aiki a jiyan ya tashi daga Ikko ne da misalin karfe 4.15 na yammacin agogon kasar zuwa Abuja wanda a yau Jumma'a 4 ga wata ake sa ran kaddamar da shi a hukumance.
An dai dakatar da zirga-zirgar kamfanin ne bayan mummuanan hatsarin da jirginsa ya yi a watan Yunin bara wanda ya tashi daga Abuja zuwa Ikko.
Kafin dawo da zirga-zirgar jiragen kamfanin Dana, kamfanoni 4 ne suka rage da suke jigila a cikin gida wato kamfanin jiragen Arik, Aero, Med-View da IRS wanda dawowar Dana suka zama 5.
Kamfanin jiragen Dana dai ta kammala duk wani gwaje-gwajen da ya kamata kafin a amince da zirga-zirgarta wanda hukumar lura da zirga-zirgar jiragen sama na kasar ta yi mata, sannan kuma aka mika mata takardun shedan yin hakan tare da izinin fara jigilar mutane.
Haka kuma kamfanin jiragen Dana ta riga ta biya diyyar kudi kimanin dalar Amurka dubu 100 ga iyalan kowane mutum da ya rasu a cikin wannan hadari na ranar 3 ga watan Yuni bara.(Fatimah)