in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta mai da hankali sosai kan cutar murar H7N9 a kasar Sin
2013-04-02 10:43:05 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ba da wata sanarwa a ran 1 ga wata cewa, hukuma mai kula da kiwon lafiya da kayyede haifuwa ta kasar Sin, ta riga ta sanar mata yanayin da Sin ke ciki, don gane da wasu mutane 3 da suka kamu da cutar murar H7N9.

Bisa sanarwar da hukumar ta kasar Sin ta bayar a ran 31 ga watan Maris, mutane 3 dake birnin Shanghai, da lardin An'hui, sun kamu da cutar munar ta H7N9. Cibiyar rigakafin cututtuka ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, wannan cuta ba ta bazu a dukkanin kasar ba.

WHO dai ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin bincike kan wannan lamari, tare da karfafa yin rigakafi, da kuma sanya ido ga wannan cuta. Ban da haka, WHO da hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin za su ci gaba da tuntubar juna kan lamarin, da kuma gabatar da karin bayyanai ga al'umma, don gane da halin da ake ciki cikin hanzari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China