2020-11-11 13:58:28 cri |
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kisan wasu kauyawa 50 wadanda 'yan bindiga suka yi a arewa maso gabashin kasar Mozambique.
A sanarwar da mai magana da yawun babban sakataren Stephane Dujarric ya fitar, mista Guterres, ya bayyana jimami game da faruwar lamarin a makon da ya gabata a lardin Cabo Delgado, inda ya bukaci hukumomin kasar da su kaddamar da bincike kan faruwar lamarin domin hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata kisan.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China