Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Mozambique zai samar da ayyukan yi masu inganci ga kasar ta nahiyar Afrika
2019-11-09 15:53:55        cri
Jakadan Kasar Sin a Mozambique Su Jian, ya ce karfafa dangantaka tsakanin Sin da Mozambique, zai samar da karin damarmakin ayyukan yi masu inganci a kasar ta kudancin Afrika.

Su Jian, ya bayyana haka ne a jiya Juma'a, lokacin da yake jawabi a bikin bada tallafin karatu na shekara-shekara ga daliban kasar Mozambique 12.

A cewarsa, la'akari da cimma matsaya guda tsakanin Sin da Mozambique kan kara karfafa dangantakarsu karkashin tsarin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", za a samu karin masu basirar iya harsuna fiye da daya, wanda zai samar da karin damarmakin ayyukan yi masu inganci ga kasar.

Jakadan ya kuma ce yana fatan tallafin zai karfafawa karin dalibai gwiwar koyon harshen Sinanci da taimakawa wajen kara inganta fahimtar juna da abota tsakanin al'ummomin kasashen 2. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China