Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon musamman na shugaban kasar Sin ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mozambique
2020-01-17 10:25:13        cri

Manzon musamman na shugaban kasar Sin kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Cai Dafeng ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Mozambique Filipe Jacinto Nyusi, da ya gudana a ran 15 ga wata a Maputo fadar mulkin kasar, sannan ya gana da shugaba Filipe Jacinto Nyusi a ran 16 ga watan.

Cai Dafeng ya ce, Sin na fatan hada kai da Mozambique don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma ingiza amincewa da juna a fannin siyasa, da habaka hadin gwiwa da kara karfafa dankon zumunci dake tsakanin jama'ar kasashen biyu, da kara taimakawa juna a harkokin kasa da kasa, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni.

A nasa bangare, Filipe Jacinto Nyusi ya ce, Mozambique na fatan shugabannin kasashen biyu, za su karfafa tuntubar juna da zurfafa hadin kansu a fannonin tsaro, tattalin arziki da cinikayya da dai sauransu, don ingiza bunkasuwar dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China