Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu mutum na farko da ya kamu da cutar COVID-19 a kasar Mozambique
2020-03-23 10:32:02        cri
Ministan lafiya na kasar Mozambique, Armindo Tiago, ya ce an samu mutum na farko da ya kamu da cutar COVID-19 a kasar.

Da yake bayyana haka yayin wani taron manema labarai da yammacin jiya a Maputo, ministan ya ce mara lafiyan dan asalin kasar ne mai shekaru 70, wanda ya koma gida daga Birtaniya a tsakiyar watan nan.

Ministan ya jaddada bukatar kiyaye matakan kariya da shugaban kasar Filipe Nyusi ya sanar, ciki har da kara sa ido da kula da tsafta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China