Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Mozambik ta yi hasashen samun karayar tattalin arziki saboda COVID-19
2020-04-03 11:07:43        cri
Firaministan kasar Mozambik Carlos Agostinho do Rosario, ya sanar a ranar Alhamis cewa, gwamnatin kasar ta yi hasashen samun karayar tattalin arziki, kana kasar za ta ci gaba da daukar jerin matakai domin rage tasirin illolin da cutar Covid-19 za ta yiwa tattalin arzikin kasar.

Rosario ya yi jawabin ne a majalisar kasar da aka gudanar a Maputo inda ya gabatar da shirin gwamnati na raya kasa na shekaru biyar tsakanin 2020-2024 ga majalisar dokokin kasar.

Firaministan ya ce annobar za ta haifar da koma baya a bangarorin kasar wanda zai shafi darajar kudin kasar, da tashin farashin kayayyakin masarufi a kasar.

Rosario ya ce, gwamnati za ta dauki matakan rage tasirin matsalolin da tattalin arzikin kasar zai fuskanta a kasafin kudinta. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China