Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Mozambique: Sojoji suna mayar da martani kan hare-haren da ake kaiwa a kasar
2020-06-01 14:12:34        cri
Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya bayyana cewa, rundunonin sojan kasar, suna daukar matakan da ya kamata kan hare-haren ta'addanci da ake kaiwa a lardin Cabo Delgado dake arewacin kasar.

Shugaban wanda ya bayyana haka, yayin da yake jawabi ta kafar rediyon kasar, yayin da ya ziyarci lardin a karshen mako, Ya ce, matakan da sojojin suke dauka suna haifar da kyakkyawan sakamako.

Ya ce, sun samu bayanan dake cewa, an kashe manyan dakarun dake adawa da gwamnati. Haka kuma fafatawar karshe da dakarun tsaron kasar suka yi tana da girma, sun kuma samu nasara. Shugaban ya ce, hukumomi na samun nasara a gundumomin Mocimboa da Quissanga da Muidumbe da kuma Macomia dake lardin Cabo Delgado, wuraren da 'yan ta'addan suke kai hare-haren

Shugaban wanda ministocin tsaro da na cikin gida suka rufa masa baya yayin ziyarar, ya kuma gana da manyan jami'an tsaron kasar dake lardin na Cabo Delgado. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China