Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta cika alkawarin kare kayayyakin al'adun tarihi na duniya
2020-11-06 14:27:04        cri
Ya zuwa karshen shekarar 2019, kasar Sin ta aiwatar da matakan kare kayayyakin al'adun tarihi na duniya har sau 726. Sabon rahoton "kayayyakin al'adun tahiri na duniya na kasar Sin na shekarar 2019" ya nuna cewa, Sin tana kokarin cika alkawuran da ta dauka yadda ya kamata.

Daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2019, sassan kasar Sin dake da kayayyakin al'adun tarihi na duniya, suna kiyaye irin wadannan kayayyaki yadda ya kamata, bisa bukatun yarjejeniyar kare kayayyakin tarihi.

Cikin wannan rahoto, an bayyana cewa, an kafa hukumomin kare kayayyakin tarihi a sassan kasar Sin, kuma kusan rabi daga cikinsu suna da hukumomin bincike kan kayayyakin tarihi, masu ma'aikata sama da dubu 36.

Bugu da kari, jarin da aka zuba a sassan kasar domin kare kayayyakin tarihi na ci gaba da karuwa, kuma a galibin sassan kasar, akwai dokoki da ka'idoji, wadanda ake bi domin kiyaye kayayyakin tarihin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China