Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fara shirin kidayar jama'a karo na 7
2020-11-02 10:05:24        cri
A jiya ne, masu aikin kidaya a kasar Sin kimanin miliyan 7, suka fara bin gida-gida don kidaya al'ummar kasar mafiya yawan jama'a a duniya karo na bakwai.

Da yake karin haske kan shirin ta kafar bidiyo, mataimakin shugaban hukumar raya kasa da yin gyare-gyare na kasar Sin Ning Jizhe, ya bayyana cewa shirin kidayar jama'ar, zai taimaka wajen sanin yawan al'umma, da tsari, da yadda za a raba albarkatu. Muhimman bayanan da za a tattara, sun hada da suna, da lambar katin shaida, da jinsi, da yanayin iyali, da matsayin ilimi, da kwarewar basine.

Shi ma mataimakin shugabar hukumar kididdiga ta kasar Sin Li Xiaochao, ya bayyana cewa, hukumarsa za ta yi kokarin ganin ta kare muhimman bayanan 'yan kasa a lokacin da ake aikin kidayar, ganin cewa bayyana muhimman bayanan mutum abu ne da aka haramta.

Bayanai na nuna cewa, tun shekarun 1990, kasar Sin ta ke gudanar da aikin kidayar al'ummar kasar bayan kowa ne shekaru goma. Kidayar da aka gudanar a baya, ta nuna cewa, yawan al'ummar kasar ya karu zuwa mutum biliyan 1.37

A wannan karo, ci gaban fasahohi da na'urorin zamani kamar wayoyin salula na zamani, manyan muhimman bayani, da manhajojin QR, suna taka muhimmiyar rawa wajen tattara da tsara yawan muhimman bayanan al'ummar dake zaune a cikin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China